27 Yuli 2021 - 15:28
Sayyid Raisi:Iran Ta Tabbatar Da Cewa Ita Kasa Ce Abin Dogaro Ga Kawayenta

Zababben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Raisi ya bayyana cewa Iran ta tabbatarwa kasashe makwabtanta kan cewa ita kasashe abar dogaro da amincewa.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto zababben shugaban yana fadar haka a ganawarsa da mataimakin firai ministan kasar Qatar da kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohamad bin Abdurrahman Al-Thani wadanda suke ziyarar a nan Teran ajiya Litinin.

Sayyid Raisi ya kara da cewa, makontan kasar Iran, sune farko a tsarin diblomasiyyar jumhuriyar Musulunci ta Iran, sannan duk wata matsala da kunno kai a tsakanin kasashen da Iran, ana iya warwaresu ta hanyar tattaunawa.

Zababben shugaban ya ce wasu kasashe ne, daga wajen yankin suke haifar da rashin jituwa da zaman lafiya a tsakanin kasashen yankin, amma babu wata matsala tsakanin kasashen da Iran.

Jami’an gwamnatin kasar ta Qatar dai sun zo kasar Iran ne don kara kyautata dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, inji mataimakin firai ministan kasar Qatar a ganawarsu da Sayyid Ra’isi.

342/